'Muna daf da kwato kudaden da aka sace'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta dauki matakan da suka dace domin kwato kudaden ta da aka sace na danyen mai.

A cewarsa sun gano bankuna da kafafen ajiyar kudade da kuma kasashen da aka ajiye kudaden da aka biya na man kasar da aka sace.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ganawarsa da wasu 'yan majalisar dokokin Amurka a ziyarar da suka kai masa a fadar Aso Rock.

Ya bayyana irin goyon baya da hadin kai da gwamnatinsa ke samu daga al'ummar kasashen waje a wurin tattaro bayannan sirri wadanda ake bukata wurin gano da samo kudaden Najeriya da aka sace.

A nasa bangaren, dan majalisa Darrel ya tabbatar wa shugaba Buhari da goyon bayan da Amurka za ta bai wa Najeriya wajen yaki da Boko Haram.