Ambaliyar ruwa a birnin Kano

Image caption An rufe wasu tashoshin mota sakamakon ambaliyar ruwa

An wayi gari ana sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Kano, inda aka kwashe sama da sa'o'i bakwai, ana ruwan, lamarin da ya janyo ambaliyar ruwa.

An samu ambaliyar, a tashoshin mota da kasuwanni, da makarantu, da kuma manyan hanyoyin birnin Kano.

Ba a samu rahoton rasuwa ba sakamakon ambaliyar ko kuma rushewar wani gida.

Jama'a da dama sun ce wannan shi ne ruwan sama mafi karfi da aka yi bana a Kano.

Wasu na cewar an shafe fiye da shekaru 10 ba a yi ruwan sama mai karfi kamar wannan ba.