An kashe dakarun Mali 10 a Timbuktu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai dubban dakarun Faransa a Mali

Rundunar sojin kasar Mali ta ce an hallaka dakarunta 10 sakamakon wani hari a barikin sojoji a yankin Timbuktu.

Wata majayar soji ta dora alhakin harin a kan kungiyar Ansar Dine mai kaifin kishin Musulunci.

Ko a ranar Asabar ma an kashe sojoji biyu a wasu hare-hare a kasar ta Mali.

Hari daga kungiyoyin masu jihadi a yanzu ya yadu zuwa wasu yankunan kudanci da tsakiyar kasar Mali.

Majalisar dinkin duniya ta ce akwai dubban dakaru na kasa-da-kasa a Mali tun lokacin da sojojin Faransa suka murkushe masu tayar da kayar baya a arewacin kasar shekaru biyu da rabi da suka wuce.