Jirgin yakin Syria ya hallaka mutane 12

Hakkin mallakar hoto AA
Image caption Mutane 12 ne suka mutu sakamakon faduwar jirgin

Rahotanni daga Syria sun ce wani jirgin yakin kasar ya fadi a wata kasuwa a yankin da ke karkashin ikon masu ta da kayar baya na Ariha, da ke arewacin kasar.

Wata majiya ta ce a kalla mutane 12 ne suka mutu sakamakon faduwar jirgin.

A lokacin da al'amarin ya faruana kai wa yankin Ariha hari ta sama, amma har yanzu ba a gano ko harbo jirgin aka yi ko kuma hatsari ya yi ba saboda wasu dalilai.

A watan Mayu ne 'yan tawaye suka kame ikon garin dai wanda yake gundumar Idlib.