Ana gwabza kazamin fada a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kashe daruruwan mutane a rikicin Yemen

Rahotanni daga Yemen na cewa ana gwabza kazamin fada domin karbe iko da wani muhimmin filin jirgin sama a arewacin birnin Aden.

Sojojin gwamnati sun ce sun sake kwato sansanin Al Anad wanda ya tawayen Houthi suka karbe a cikin watan Maris.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da sake kwato sansanin, kuma wani rahoto ya ambato 'yan tawayen na cewa har yanzu su ke rike da shi.

Wakilin BBC ya ce, "wannan shi ne hari mafi girma da dakarun da ke goyon bayan gwamnati suka kai, kuma daya daga cikin kwamandodjinsu ya dage cewa sun yi nasarar korar 'yan tawayen".

Wata majiya ta ce dakarun gwamnatin sun gamu da tirjiya daga 'yan tawayen don haka ba su yi wata gagaruwar nasara ba.