An nada sababbin shugabanni a NNPC da NCC

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Ana zargin NNPC da tafka cuwa-cuwa

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya sanar da nadin Dr Emmanuel Ibe Kachikwu a matsayin sabon shugaban kamfanin mai na kasa NNPC.

Kafin nadin na sa, Dr Kachikwu shi ne mataimakin shugaban kamfanin mai na Exxon-Mobil mai kula da nahiyar Afrika.

Dr. Kachikwu ya maye gurbin Dr. Joseph Thlama Dawha.

Sabon shugaban man na NNPC, dan asalin jihar Delta ne.

Haka zalika shugaban na Nigeria ya sanar da nadin Farfesa Umaru Garba Danbatta a matsayin sabon shugaban hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta kasar NCC.

Farfesa Danbatta ya maye gurbin Dr. Eugene Juwah.