Siyasar Mangwaro tsakanin India da Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Pakistan ce ta biyar a duniya a noman Mangwaro.

Ga ala'ada a kasashen kudancin Asiya, duk shekara shugabannin Pakistan na aika wa takwarorin su a India Mangwaro.

Duk da shaharar siyasar Mangwaron, dangantaka tsakanin kasashen da ke mabwabtaka da juna ta yi tsami.

Rahotanni sun nuna cewa, makonnin da suka gabata a lokacin bikin sallar idi, Firayi Ministan Pakistan Nawaz Sharif ya aika wa Firayi Ministan India, Narendra Modi kwalin Mangwaro.

Duk da haka babu jituwa a tsakanin su.

An aiko da goron sallar, duk da cewa ana ta faman yaki tsakanin Indiya da Pakistan a yankin Kashmir inda aka kashe a kalla mutane biyar.

"An aiko wa Mr Modi Mangwaro ta hannun jami'an Pakistan, duk da kasar ta zargi Indiya da kai farmaki a sararin samaniyarsu," In ji wani jami'in Indiya a jaridar The Hindustan ta kasar.

Mr Sharif ya aikowa Mr Modi kilo 10 na Mangwaro, kilo 15 ga Shugaban kasar Indiya Pranab Mukherjee da kuma kilo goma goma ga tsofaffin Firayi Minista Atal Behari Vajpayee da Manmohan Singh.

'Goron Sallah'

Amma wannan siyasa ta Mangwaro bata yi farin jini ba, saboda ba ta gyara dangantakar tsakanin kasashen ba.

A ranar Litinin ne Indiya ta dorawa Pakistan alhakin wani hari da aka kai a wata motar bas da kuma ofishin 'yan sanda a garin Gurudaspur da ke arewacin jihar Punjab, inda mutane goma tare da wani babban jami'in tsaro suka hallaka.

A farkon watan da ya gabata ma sojojin Pakistan sun ki amsar kyautar sallah daga sojojin Indiya a dalilin rashin jituwar ta su.

Kyautar kayan zaki a tsakanin kasashen a lokacin bukukuwa ya zamo ala'ada, kamar kyautar Mangwaro, amma ita Indiya bata maida tukuici da Mangwaro.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Indiya ta fi kowace kasa a duniya noman Mangwaro amma bata ba da shi a matsayin tukuici ga makwabciyar ta Pakistan.

Pakistan ce ta biyar cikin kasashe a noman Mangwaro kuma wasu kafofin sun bayyana cewa ba Indiya kadai ta ke turawa ba, ala'adar kasar ce ta aikawa shugabannin kasashe Mangwaro.

Indiya ce ta fi kowace kasa a duniya noman Magwaro, duk da cewar akwai musu tsakanin kasashen a kan ko ta wace kasa ce ta fi kyau.

"Zai yi kyau Indiya ita ma ta turawa shugabannin Pakistan Mangwaro," In ji wani dan siyasar Indiya Mani Shankar Aiyar

"Nayi aiki a ofishin jakadancin Indiya a kasar Karaci, kuma na san Mangwaron Pakistan ta fi ta Indiya."

Yawancin 'yan kasar Indiya suna alfahari da Mangwaron da ake nomawa a kasar su, saboda haka baza su yarda da zancen Mr Aiyar ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Modi ya karbi gayyatar da Mr. Sharif ya yi masa na ziyartar taron yankuna da za ayi a Islamabad a badi.

Ayesha Siddiqa, wata mai sharhi aka harkar diflomasiyya ta yi na'am da zancen Mr. Aiyar, inda ta ce, "Mangoro da wasan Kurket sune dabaru mafi dadewa da ake amfani dasu wurin daidadita siyasa a tsakanin Indiya da Pakistan, kasashen biyu basa maganar baka da juna."