Sojoji sun kwance bama-bamai a Gwoza

Hakkin mallakar hoto nig
Image caption Wasu kenan daga cikin ababan fashewar da rundunar ta kwance

Runduna ta 7 ta sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, ta ce ta samu nasarar kwance bama-bamai guda biyar da 'yan kungiyar Boko Haram suka dasa a kan titin da ya hada garin Gwoza da Yamteke, a jihar Borno.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, kanal Sani Usman Kuka-sheka, ya fitar ta ce injiniyoyin rundunar ne suka kwakkwance bama-baman kafin daga bisani suka lalata su.

Kazalika, sanarwar ta kara da cewa sojojin sun sami muggan makamai tare da kayan hada bama-bamai a wata maboya a garin Dikwa, kwanaki kadan bayan da sojojin suka fatattaki 'yan Boko Haram daga garin.

Rundunar ta kuma lashi takobin kawo karshe ayyukan ta'addanci daga arewa maso gabashin kasar.