'Yan Biritaniya na bukatar sinadarin bitamin D

Image caption Likita zai iya bayar da Bitamin D kuma za'a iya saya a manyan kantuna

Masana a gwamnatin Biritaniya sun ce ya kamata 'yan kasar su dinga shan sinadarin bitamin D domin maye gurbin karancin sinadarin saboda rashin hasken sosai a Ingila.

Kwamitin kimiya da ke ba da shawarwari a kan ka'idojin abinci mai gina jiki da aka kafa, ya bayar da shawarar cewa, ya kamata mutum ya tabbatar da cewar yana shan maunin microgram 10 na sinadarin bitamin D daga shekarar haihuwa domin tabbatar da mutane sun samu isashe.

Yanzu ana shawarwari a kan tsare-tsare har zuwa 23 ga watan Satumba.

Wadanda suke cikin hadari su ne masu juna biyu da yara wadanda suke kasa da shekaru biyar da kuma wadanda suka wuce shekaru 65 - ya kamata su rika shan sinadarin.

Amma saboda babu wata hanya mai sauki da ake tantance wanda ya ke samun isashen sinadarin Bitamin D, hukumar SACN ta bayar da shawara kowa ya sha sinadarin saboda amfanin da zai kawo.

An yi la'akarin cewar hadarin da ke tare da samun bitamin D dayawa a jikin mutun kadan n

'Lokacin hunturu'

Cibiyar samar da kyakyawar lafiya da kulawa ta kasa, wadda ke bayar da shawarwari ga shirin samar da lafiya na kasa a kan magani, ya riga ya nemi a rika bayar da sinadarin Bitamin D a yakuna da dama saboda a shawo kan annobar karancin sinadarin.

Kiyasin da hukuma ta fitar na nuna daya a cikin mutane biyar da daya a cikin yra shida a Ingila, akwai yuwar suna da karanci sinadarin.

Mutane da dama suna samun sinadarin a fatar su ne ta hanyar hasken rana.

Amma kuma adadin wanda ya ke cikin abincin kadan ne, sabanin wasu sinadaran.

Karancin hasken rana a watannin hunturu na nufin mutane a Ingila suna cikin hadari.

Ka'idojin hukumar samar da lafiya da kulawa ta kasa ya nemi a bayard a sinadaria kyauta kuma manyan kantuna su sayar da su a farashi mai rahusa.

Karancin sinadarin na iya janyo rashin kwarin kashi.