Dakarun Yemen sun kwace filin jirgin sama

Image caption An dade ana yakin basasa a Yemen

Dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen sun ce sun kori 'yan tawayen Houthi a muhimmin filin jirgin sama da ke kudancin kasar.

Dakarun gwamnati da kawayensu sun kaddamar da gagarumin hari da zummar kwato sansanin na Al-Anad , kuma yanzu sun ce ya fada hannanusu.

Wasu hotunan bidiyo sun ce yadda aka rika ba-ta-kashi tsakanin banagarorin biyu, kuma daga bisani dakarun gwamnatin Yemen din sun yi ta murna bayan samun nasara:

A kwanakin baya ne wata rundunar soji da kasar Saudiyya, wacce ke goyon bayan gwamnatin Yemen ke jagoranta, ta karawa dakarun manyan makamai domin su fafata da yan tawayen.

Ana zargin kasar Iran da taimaka wa 'yan tawayen wadadan galibinsu 'yan shi'a ne.