'Karuwar kashe mata da yara a Afghanistan'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matan Afghanistan.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu karuwar mata da yara da aka kashe ko aka raunata a Afghanistan tun lokacin da dakarun NATO suka janye a watan Disambar bara.

A cikin wani rahoto, Majalisar ta bayyana cewa daukacin wadanda abin ya shafa a watanni shida sun kai kaso daya cikin su dari, amma yanzu matan da aka kashe ko aka raunata sun karu har sun kai kaso 23 cikin 100.

Yaran da yakin ya shafa kuma sun kai kaso 13 cikin dari.

An ce an samu karuwar ce sakamakon fada da ake yi a kasa da ya maye gurbin dasa bama-bamai a gefen titi.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kungiyar Taliban da sauran kungiyoyin masu adawa da gwamnati, da su daina harin fararen hula.

A kalla mutane 600 ne suka hallaka, kuma an raunata mutane sama da 3,000 a Afghanistan cikin watanni shidan da suka gabata.