'Yan Boko Haram sun bindige masunta tara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta tafka ta'asa sosai a Nigeria

Rahotanni daga jihar Borno a Nigeria na cewa 'yan Boko Haram ne sun bindige wasu masunta tara har lahira a kusa da tafkin Chadi.

Lamarin ya auku ne a ranar Talata, yayinda masuntan ke kan hanyarsu ta zuwa Baga daga Munguno.

Alhaji Abubakar Gamandi, shugaban kungiyar masu sayar da kifi a garin Baga na jihar ta Borno, ya tabbatar wa BBC afkuwar lamarin.

A cewarsa 'yan Boko Haram din sun fitar da masuntan daga cikin motarsu kafin su harbe su.

Gamandi ya kara da cewar daga bisani sojoji sun fatattaki 'yan Boko Haram din inda suka hallaka mayakan 13.