Indiya za ta sake bude shafukan batsa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Indiya ta sake bude shafukan batsa na intanet

Gwamnatin Indiya ta ce za ta sake bude shafukan intanet fiye da 800 na batsa, bayan da rufe shafukan ya jawo ce-ce-kuce a kasar.

Masu sukar lamiri sun zargi gwamnatin da sa ido a lamarin da bai shafeta ba.

Amma gwamnatin ta ce ta yi hakan ne domin kare yara daga shiga shafukan batsar domin gudun lalacewar tarbiyarsu.

Jami'ai dai sun ce sauran shafukan da suke nuna batsar yara za su ci gaba da kasancewa a rufe.

A makon da ya gabata ne gwamnati ta bai wa kamfanonin da ke samar da hanyoyin sadarwa umarnin rufe dukkan shafukan da ke nuna batsa, domin samar da kyakkyawar tarbiya a tsakanin al'umma.