Jiragen kasa biyu sun yi hadari a India

Image caption Jiragen kasa da suka yi hadari a India

Akalla mutane sha tara ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama suka jikkata a kasar India, sakamakon hadarin jiragen kasa guda biyu.

An dai ce jiragen sun kauce daga kan layin dogon ne a kokarin ketare wata gada da ke saman kogi, a inda igiyar ruwa ta make su.

Yanzu haka masu aikin ceto suna can suna ta faman kokarin ceton mutane amma kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya da rashin kyawun yanayi suna kawo cikas ga aikin ceton.

Jirgin dai ya hau kan wata gada dake saman kogi a jihar Madhya Pradesh dake tsakiyar India ne.

Wasu sassan da fasinja suke sun afka cikin kogi.