Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shekaru 70 da kai harin Hiroshima

Ranar Alhamis ne ake cika shekaru saba'in da kai harin nukiliya na farko a duniya. Amirka ce ta jefa bam din a birnin Hiroshima na Japan, a 1945. Mutane dubu dari da arba'in ne suka hallaka, daga cikin dubu dari uku da hamsin din da ke zaune a garin. BBC ta zanta da Bun Hashizume, wadda tana da shekaru goma sha hudu a lokacin da bam din nukiliyar ya fashe. Ga dai labarinta: