An kai harin kunar bakin wake Saudiya

Hakkin mallakar hoto saudi IS

Wani dan kunar bakin wake ya tada bam a wani masallaci da ke yankin Aseer na kasar Saudiya.

A kalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu kuma sama da mutane 20 ne suka jikkata.

Al'amarin ya faru ne kusa da wani sansanin sojoji da ke kusa da kan iyakar kasar Yemen.

Zuwa yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.