An kalubalanci Shell kan malalar mai

Hakkin mallakar hoto

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta yi kira ga kamfanin mai na Shell da ya kara azama a kokarin da ake yi na share dagwalon danyen man da ya malala a yankin Ogoni na Naija Delta a Nigeria.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a tsokacin da ta yi kan matakin da shugaban Najeriyar ya dauka na gaggauta aiwatar da rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan share dagwalon danyen mai da ya malala a yankin.

Al'ummomin Ogoni na zargin kamfanin na Shell da yin sakaci wajen haddasa malalar mai a yankinsu, sai dai kamfanin ya ce barayin mai ne suka fasa bututunsa da ya haddasa lamarin.

Kamfanin ya kuma ce yana ci gaba da sake duba yadda zai inganta yanayin share danyen man da ke malala kamar yadda duniya ta yarda da shi.