Biyan kudin sadaki a Afrika

Hakkin mallakar hoto AFP

Wata kotu a kasar Uganda ta yanke hukuncin cewar sadaki ya halatta a shari'ance.

Amma alkalan sun haramta mai do da sadaki bayan aure ya mutu.

Biyan sadaki al'adar Afrika ce, duk da al'adun sun bambanta, ga wasu ma'aikatan BBC nan da karin bayani akan al'adar sadaki a kasashen su.

Pumza Fihlani, Afrika ta Kudu:

A Afrika ta Kudu, ana kiran sadaki "Lobola", inda dangin ango suke bai wa dangin amarya kyautar kudi ko shanu ko ma duka biyu, wanda hakan zai nuna yana son 'yar su da aure.

Loloba wani alamu ne na cewa angon a shirye yake ya kula da amaryarsa, kuma hakan yana nuna daukaka al'adu ne ba wai ko an maida ta haja ba.

Kim Chakanetsa, Zimbabwe:

"Loloba" sunan da ake kiran sadaki ke nan ma a kudancin Zimbawe, amma a tsakanin kabilar Shona ana ce da shi "roora", kuma suma a ala'adance suna bayar da shanu, amma yanzu ana bayar da kudin shanun ne, bayan an tsadance.

Akwai al'adun toshi daban-daban, amma duk ana yin su ne domin a nuna wa dangin amarya ana godiya da tarbiyyar da suka bai wa 'yar su, ba wai ana yin su ne domin a saye ta ba.

Abdourahmane Dia, Senegal:

Biyan kudin sadaki yana cikin al'adar kasar Senegal, amma shaidar aure ce.

Kudi kalilan ake bai wa dangin amarya da goro a Masallaci, bayan haka sai wasu kudade da ake bayarwa daga kasa da dala 100 har ma dubbannin daloli.

Angela Ngendo, Kenya:

Kundin tsarin mulkin Kenya ya haramta bayar da sadaki, amma idan akwai fahimtar cewa ana biya.

Ana biyan sadaki da shanu a tsakanin makiyaya duk da ana sukar wannan dabi'ar da cewa hakan yana janyo satar shanu, amma kuma wasu al'ummar suna karbar kudi.

Hakan yana sa mutane cikin alhinin cewa an sayar da amaryar ne.

Leone Ouedraogo, Burkina Faso:

Dabi'ar biyan sadaki ba tilas ba ne a kasar, kuma kabilar Burinabe ne suka fi biya.

Ba a kayyade kudin ba kuma ana iya biyan kudi kalilan, amma an fi bayar da goro da kayan shaye-shaye da taba, wasu kabilun ma har da Akuya suke bayarwa.

Dangin amarya dai ba sa matsawa a kan sadaki.

Aichatou Moussa, Niger:

A jamhuriyar Nijar, gwamnati ta kyasta sadaki Cefa dubu 50 (watau dala 54 ko Euro 54), amma akwai masu biyan fiye da haka.

Akwai yarjejeniya a tsakanin dangin amarya da ango, amma sadakin an dauke shi a matsayin shaida ce kawai ta daurin aure ba wai a kan an sayi mace ba, saboda haka ma mutanen Nijar ke jaddada cewar babu kudin da zai iya sayan mutum.