"Fim din Gwaska zai zama zakaran gwajin dafi"

Hakkin mallakar hoto Adam zango
Image caption Fim din Gwaska na Adam Zango

An yi nunin wani bangare na wani sabon fim din Hausa mai suna Gwaska, wanda shahararren jarumin nan Adam Zango ya jagoranta.

Masu ruwa da tsaki a harkar fina-finan Hausa ne dai suka taru dan kallon fim din da kuma bayar da shawarwari ta yadda za a inganta fim din, wanda suka ce ya zama wani zakaran gwajin dafi a fina-finan Hausa.

Masu shirya fina-finan Hausa da jarumai da suka halarci nunin fim din na cewa fim din Gwaska ya zame musu kalubale, kuma ya tashe su tsaye.

A baya dai an sha sukar masu shirya fina-finan Hausa da cewa suna yin fina-finan da basa kan tsarin al'adu irn na Hausawa.