An kai hari kan wani otal a Mali

Image caption Sojojin wanzar da zaman lafiya a Mali

Wasu 'yan bindiga a Mali sun kai hari kan wani otal dake tsakiyar garin Sevare.

Jami'an majalisar dinkin duniya da kuma sojoji sun ce a wata musayar wuta da akayi tare da jami'an tsaro, an kashe akalla mutane takwas, biyar daga cikin su sojoji ne daya kuma jami'i ne na majalisar dinkin duniya yayin da sauran biyun kuma 'yan bindiga ne.

Hukumomin kasar ta Mali sun ce har yanzu akwai wani dan kasar Rasha da kuma wasu 'yan kasar Afrika ta kudu su uku a cikin otal din wadanda 'yan bindigar suke rike da su.

Yawanci dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya ne dai ke amfani da otal din.

Kazalika rahotanni sun ce wani dan kasar Ukraine ya tsallake rijiya da baya a lokacin da ake gwabzawar.