An zurfafa bincike don gano jirgin MH370

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani bangare na jirgin MH370

Faransa ta tura wani jirgi mai saukar ungulu na bincike da kuma wasu kwale-kwale zuwa kusa da tekun Indiya, a wani mataki na kara samun sauran tarkace na bangaren jirgin Malaysian nan na MH370 da ya yi batan dabo.

Tuni aka bukaci hukumomi a tsibiran da ke makwabtaka da tekun da su dudduba bangarorin su.

A China, wasu daga cikin iyalan fasinjojin da ke cikin jirgin na MH370 sun gudanar da zanga-zanga a kofar ofishin jirgin da ke Beijing.

Ministan harkokin wajen China Wang Yi, ya shaidawa manema labarai cewa ya kamata Malaysia ta rinka sanar da iyalan wadanda ke cikin jirgin da ya bace duk halin da ake ciki.

Ya ce "muna ta jin labarai kana muna sanya idanu a kan halin da ake ciki."

Mista Wang Yi ya kuma shawarci Malaysia da ta kara yi wa iyalan fasinjojin cikin jirgin cikakken bayani a kan ci gaban da ake samu game da neman jirgin.