Nigeria za ta soma kera manyan makamai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Nigeria sun shafe shekaru shida suna yaki da Boko Haram

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce kasar na shirin soma kera makamai domin dakarunta saboda a rage dogaro da makamai na kasashen waje.

"Mun umurci ma'aikatar tsaro ta fitar da tsari domin gina masana'antar samar da makamai a Nigeria," in ji Buhari.

Buhari ya kara da cewar zai yi wa kamfanin makamai na Kaduna watau DICON wanda aka kafa a shekarar 1964 garambawul domin soma aiki gadan-gadan.

Wata sanarwa da kakaki shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar ta ce gwamnatin kasar za ta fitar da tsare-tsare domin ganin masana'antar ta koma ta zamani.

DICON a yanzu na kera kananan bindigogi ne da kuma wasu 'yan abubuwa na aikin farar- hula.

Dakarun Nigeria na bukatar makamai na zamani domin yaki da kungiyar Boko Haram wadda ta hallaka dubban mutane da kuma raba wasu fiye da miliyan daga muhallansu.