An koka kan satar fasahar fina-finai

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Satar fasahar fina-finai ta yi kamari a Najeriya

Wasu masu harkar shirya fina-finai da mawaka a Najeriya,sun koka game da karuwar matsalar satar fasaha a harkar shirya fina-finai a kasar.

Sun kuma bukaci hukumomin kasar da su samar da hukunci mai tsanani ga duk wanda da aka samu da laifin satar fasaha.

Chief Tony Okoraji, shi ne shugaban kungiyar da ke yaki da masu satar fasahar mallaka a Najeriya COSAN, ya ce wannan matsala tana matukar shafar tattalin arzikin kasa.

Rahotanni sun ce a Najeriya ana asarar kimanin Naira biliyan shida a kowace shekara a kan satar fasaha da ake tafkawa a kasar.