"Babu hannayenmu a kisan sojoji"

Sooji Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar sojin Najeriya na guduar da bincike akan harin a da ya hallaka sojoji 4 da dan sanda 1 a Nembe jihar Bayelsa

Shugabannin al'ummar yankin Nembe na jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya sun ce ba su da hannu a kisan da aka yi wa wasu sojoji ranar Jumma'a.

Wasu daga cikinsu sun shaida wa BBC cewa harin ya girgiza su ya kuma sa su cikin zaman zulumi.

Dattawan sun yi kiran taro na gaggawa domin tattuana wa a kan yadda za su bayar da tasu gudunmawar wajen gano wadanda suka yi wanna aika-aika.

Shaidu sun ce sojoji hudu aka kashe da kuma dan sandan kwantar da tarzoma guda daya.

Kakakin rundunar sojoji da ke yankin, Laftanar Kanar Ado Isa, ya tabbatar wa BBC aukuwar lamarin amma ya ce suna nan suna gudanar da bincike.

Sai dai bai ce komai ba game da wadanda aka kashe.

Yawancin arzikin Najeria dai daga yankin na Niger Delta ake samo shi.

Masu fafutika daga yankin sun rika kai hare-hare a tsakanin 2002 zuwa 2009 domin, a cewar su, an talauta yankin an kuma bata muhalli.