Gwamnatin Iraqi za ta yi sauye-sauye

Firaiministan Iraqi Haidar al-Abadi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Iraqi na fuskantar barazanar masu tada kayar baya na kungiyar IS.

Firaministan Iraki, Haidar Al Abada ya bayyana gagaruman sauye-sauye da ke da nufin rage kashe kudi da gwamnati ke yi da kuma yaki da cin hanci. Matakan sun hada da soke mukaman mataimakin shugaban kasa da na firaminista.

Daya daga cikin mataimakan shugaban kasa su ukku shi ne abkin hamayyar Firaministan Abadin, wato Nuri Al - Maliki. Haka kuma Firministan ya ce bai kamata nan gaba a yi la'akari da jam'iyya ko mazhaba ba wajen nada manyan mukamai.

A yanzu dai abinda ke gaban Mr Abadi shi ne ya yi kokarin aiwatar da abubuwan da al'umar kasar ke bukata ciki kuwa har da kawo karshen mayakan da ke ikirarin kafa daular musulunci.

Kasar Iraqi dai ta shiya rikita-rikitar siyasa ne tun bayan juyin-juya halin da ya hambarar da gwamnatin Marigayi Saddam Hussein, kuma tun da ga wanna lokaci tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa da ta'addanci suka mamaye kasar.