Yoyon fitsari na addabar mata 800,000 a Najeriya

Image caption Mata a Uganda ma suna fama da ciwon yoyon fitsari

A Najeriya, har yanzu ana fama da matsalar yoyon fitsari, wadda ke jefa masu fama da larurar cikin kunci sakamakon kyamar su da wasu ke yi a tsakanin al'umma.

Wasu alkaluma daga sashen kula da al'umma na majalisar dinkin duniya na cewa akalla mata 800,000 ne ke fama da cutar.

Da ma dai hukumomi da kuma wasu kungiyoyi sun dukufa wajen yaki da cutar ta hanyar kula da majinyatan da wayar da kan al'umma.

Dr Adamu Isa kwararren Likitan yoyon fitsari ne, kuma jami'i ne na Fistula Care Plus, wani sashe mai yaki da cutar, da ke karkashin kungiyar USAID, ya kuma shaida wa BBC cewa har yanzu ana fama da wannan matsala a Najeriya.

Sai dai ya ce watakila adadin masu fama da cutar bai kai alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ke ikirari ba.

Alkaluman dai sun nuna kashi 40 bisa 100 na masu fama da cutar sun fito ne daga Najeriya.

Likitoci sun ce auren kuruciya da rashin kulawar kwararru ga masu juna biyu na daga cikin matsalolin da ke haddasa cutar yoyon fitsari.