DakarunYemen sun karbe birnin Zinjibir

Mayaka 'yan tawayen Houthi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar yemen ta shiga rikicin siyasa tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Ali Abdallah Saleh.

Dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen da taimakon hari ta sama na kawance da kasar Sa'udiyya ke jagoranta, sun kama birnin Zinjibar da kudancin kasar, daga 'yan tawaye 'yan Houthi da kawayensu.

Zinjibar shi ne babban birnin lardin Abyan, kuma wurin da aka yi faman gumurzu a cikiin 'yan kwanakin da suka shiga.

Rasa birnin babban koma-baya ne ga 'yan tawayen, abin da ya biyo bayan sake kwace birnin Aden, na biyu mafi girma a kasar da aka yi daga hannunsu a watan jiya.