Hanyar jihohin Zamfara da makwabta ta datse

Gadar Danmarke

Daruruwan matafiya da ababen hawansu sun rasa na yi a kan babbar hanyar da ta hada jihohin Zamfara da makwabtanta, wato Sakkwato da Kebbi sakamakon ruftawar da wata gada ta yi a kan hanyar.

Gadar -- wadda aka fi sani da gadar Danmarke, ta auka ne bayan sa'o'in da aka kwashe ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin.

Wannan lamari dai, kamar yanda wasu matafiya suka shaida wa wakilin BBC, ya tilasta wa wasu komawa da baya, yayin da kan wasu fasinjoji ya daure, suka rasa inda za su sa kansu.

Bincike dai ya nuna cewa gadar ta dade da nuna alamun za ta karye, amma mahukunta ba su gaggauta daukar matakin gyara ta ba.

Al'ummar yankin sun bukaci gwamnatin da lamarin ya shafa, kama daga gwamnatocin jihohin yankin zuwa ta tarayya da su hanzarta kai musu dauki ta hanyar sake gina gadar.

Wannan hanyar dai tana da muhimmanci idan aka yi la'akari da dimbin jama'ar da ke zirga-zirga a kan ta.