Buhari ya kafa kwamitin yaki da rashawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Buhari ya ce gwamnatinsa za ta hukunta masu almundahana

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya nada wani kwamitin da zai ba shi shawara kan yadda zai yaki cin hanci da rashawa.

Kwamitin, wanda ya kunshi masana, zai rika bai wa gwamnatin kasar shawara kan yadda za ta yi yaki da almundahana da ta yi wa kasar kanta da kuma aiwatar da gyare-gyare a fannin shari'ar kasar.

A sanarwar da ta fito daga kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, ta ce kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Farfesa Itse Sagay.

Wasu gidauniyoyi uku watau Ford Foundation da MacArthur Foundation da kuma Open Society Foundation ne za su dauki nauyi kwamitin inda ya kebe dala miliyan biyar.

Sauran 'yan kwamitin sun hada da;

  1. Prof. Femi Odekunle
  2. Dr. (Mrs) Benedicta Daudu
  3. Prof. E. Alemika
  4. Prof. Sadiq Radda
  5. Hadiza Bala Usman da kuma
  6. Prof. Bolaji Owasanoye