Buhari ya yi gargadi kan kudaden bashi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Buhari ya sha alwashin kawar da cin hanci a Nigeria

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya bukaci ma'aikatar kudin kasar ta yi karin bayani kan kudin da aka karbo bashi na ayyukan sufurin jiragen kasa, aka kuma karkatasu zuwa wasu ayyukan.

Shugaban ya ce abin takaici ne a karbo bashi daga kasar waje sai kuma a karkata kudin zuwa wasu ayyukan da ba sa cikin yarjejeniyar da aka kula yayin karbo bashin.

Sanarwa da kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce abin damuwa ne a ce a kasa kamalla wasu gine-ginen gwamnati saboda karkatar da kudaden da aka karbo a matsayin bashi daga kasashen waje.

"Dole ne a bi ka'ida wajen daukar kudi daga wasu ayyuka, sannan a karkatar da su zuwa wasu ayyukan," in ji Buhari.

Shugaban na mai da martani ne kan yadda aka karkatar da kaso mai tsoka daga bashin dala biliyan daya da aka karbo daga bakin China domin gina layin jirgin kasa na zamani daga Lagos zuwa Kano, sai aka tura kudin zuwa gudanar da wasu ayyukan.