'Yan sandan Kamaru sun ceto yara 70

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru na cikin kawance yaki da Boko Haram

'Yan sanda dauke da makamai a Kamaru, sun kai samame a wani gida inda suka kwato wasu yara kimanin saba'in wadanda ake tsare da su.

Wasu daga cikin yaran sun shafe fiye tsawon shekaru uku cikin sarka.

Gidan da aka kwato yaran, wanda ke wata unguwa a Ngaoundere da ke yankin arewacin kasar, mallakin wani malami ne da ke karantar da Alkurani.

Rahotannin da ke fitowa daga kafofin watsa labarai na cikin gida, na nuna cewa, malamin ya ce, iyaye ne da kansu ke tura mai 'ya'yansu don ya horar da su.

Yawancin yaran dai na cikin wani mawuyacin hali.