EU ta hana shigar da kayan abinci daga Nigeria

Image caption EU ta hana Najeriya shigar da kayan abinci kamar su busasshen kifi zuwa Turai

Masana Tattalin arziki a Najeriya sun bayyana cewa tattalin arzikin kasar na fuskantar barazana bayan matakin da Kungiyar Tarayyar Turai EU, ta dauka na haramta shigar da kayyakin abinci da suka hada da busashen kifi da nama da man kade daga Najeriyar zuwa nahiyar Turan har zuwa shekarar 2016.

A sanarwar da ta fitar, EU ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda yawan magungunan kashe kwarin da ke kunshe cikinsu.

Masanan sun ce matakin EU na zuwa ne yayin da Najeriyar take kokarin bunkasa harkokin kasuwancin fitar da kayayyakinta da kuma habaka bangaren ayyukan gonarta da kuma samar da ayyukan yi.

A makon da ya gabata ne kungiyar Tarayyar Turan ta sanar da daukar wannan matakin.