Tattaunawa kan rikicin kasar Libya

Asalin hoton, Reuters
Al'ummomin kasar Libya
A yau ne ofishin Majalisar Dinkin Duniya ke karbar bakuncin wata sabuwar tattaunawa a Geneva kan kasar Libya.
Hakan na zuwa ne yayin da kasashen duniya suka sake wani sabon yunkuri na kammala wata yarjejeniya ta kafa wata gwamnatin hadin kai a Libyar.
Tun watan Janairu ne dai ake tattaunawa kuma gwamnatocin kasashen Yamma na fatan wannan tattaunawar ta baya- bayan nan za ta bada damar masu ruwa da tsaki a rikicin kasar su warware banbance banbancen dake tsakanin su.
Idan aka yi la'akari da irin labarun da ake samu na rashin kwanciyar hankali a Libya tun lokacin mutuwar tsohon shugaban kasar Kanal Gaddafi, za a iya cewa babu wani wanda ke kokarin sasanta rikicin siyasar da ake fuskanta a kasar.