Sojoji sun kama mutane 6 a Niger Delta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yankin Niger Delta yana da albarkar man fetur a Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama mutane shida a yankin Niger Delta, a wani martani na harin da aka kai wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji da 'yan sanda hudu.

Rundunar sojin ta ce ta gano makamai da harsashai masu yawa da kuma kananan jiragen ruwa a lokacin da ta kai wani samame a sansanin masu tayar da kayar baya.

Rundunar sojin ta kuma ce tana ci gaba da neman sauran wadanda ake zargi da aikata laifin.

A baya dai masu tayar da kayar baya a yankin Niger Delta sun sha fada da gwamnati har zuwa shekarar 2009 da aka sasanta.