An hana wasu matasan Nigeria barin kasar

Masu yiwa kasa hidima (NYSC)  a Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu yiwa kasa hidima (NYSC) a Nigeria

Hukumar shige da fice ta Najeriya wato Immigration, ta ce a cikin watanni 15 da suka wuce ta hana matasa sama da 23,000 barin kasar.

Hukumar ta ce ta yi hakan ne bisa fargabar cewa matasan za su iya aikata ta'adanci ko karuwanci da kuma sauran ayyukan ashsha a kasashen waje.

Immigration ta kara da cewa za ta ci gaba da amfani da matakai masu tsauri wajen tantance wadanda suke son su yi tafiya zuwa kasashen ketare.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana daukar matakai na ganin an kawo karshen hare-haren ta'addanci a kasar.