Abin da ya sa na fara Nollywood — Rahma Sadau

Rahma ce ta biyu a bangaren mata a Kannywood da ta shiga Nollywood

Asalin hoton, Rahma Sadau

Bayanan hoto,

Rahma ce ta biyu a bangaren mata a Kannywood da ta shiga Nollywood

Jarumar fina-finan Hausa, Rahma Sadau, ta ce ta fara fitowa a fina-finan kudancin Najeriya da aka fi sani Nollywood ne domin ta inganta sana'arta da kuma kara ilimi.

Jarumar ta shaida wa BBC cewa a matsayin ta na matashiyar 'yar fina-finai, tana da muhimmiyar rawa da za ta taka wajen wayar da kan jama'a.

Ta ce "Da ma ina neman dama ne, kuma na samu shi ya sa na fara fina finan Nollywood. Kar ka manta ni dama so nake na zama jaruma ba wai kawai ta fina finan Hausa ba, don haka a shirye nake na taka rawa a kowanne fim."

A cewar ta, ba ta fuskanci wani kalubale ba tun da ta fara fim din saboda kusan duk abin da ake yi a fina fina Hausa, wato Kannywood, ana yin su a Nollywood.

Sai dai ta ce ba za ta taka wata rawar da ta sabawa addini ko al'adarta ba, tana mai cewa yawancin rawar da za ta taka za ta taka ta shafi irin wacce Hausawa za su fito a cikin fim ne.

Ta yi kira ga mutanen da ke sukar ta a kan shiga Nollywood da cewa su sauya matsayi domin ba ta shiga harkar domin ta yada ko koyi miyagun halaye ba.

Rahma ta ce za ta fito ne a wani fim na Ingishi da ake kira 'The Light Will Come'.

Jaruman da za ta fito tare da su sun hada da Majid Michel, Mercy Johnson.

Jaruma fina-finan Hausa maza irin su Ali Nuhu da Sani Danja ne ke fito a fina-finan na Nollywood.