Motoci sun soma wucewa ta gadar Danmarke

Image caption Rugujewar gadar ta janyo tsaiko a harkokin zirga-zirga

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce an soma zirga-zirga kamar yadda aka saba tsakanin jahar da makwabtan jihohin Sakkwato da Kebbi bayan wani gyaran wucin gadi da ta sa aka yi wa gadar da rufta a ranar Lahadi.

Mukaddashin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Wakkala ya shaida wa BBC cewa motoci na bin hanyar kamar yadda aka saba ne bayan cike kwazazzabu da manyan duwatsu da karafa da wasu injiniyoyi suka yi.

Gadar -- wadda aka fi sani da gadar Danmarke, ta auka ne bayan sa'o'in da aka kwashe ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin.

Bincike dai ya nuna cewa gadar ta dade da nuna alamun za ta karye, amma mahukunta ba su gaggauta daukar matakin gyara ta ba.