Shekara guda ba cutar Polio a Afrika

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A Somaliya ne aka samu mutum na karshe da cutar Polio ta kama a bara

A ranar Talata ne nahiyar Afrika ta cika shekara guda cif ba tare da an sake samun sabuwar matsala ta cutar shan-Inna ba wato Polio.

A kasar Somaliya ne aka samu wanda cutar ta kama na karshe a bara.

Najeriya kuwa, tun a watan da ya gabata ta cika shekara guda cif ba tare da an sake samun sabuwar matsala ba.

Amma masana sun nuna damuwarsu kan rikice-rikice da ake fama da su a arewa maso gabashin kasar da cewa barazana ce sosai ga dakile cutar a yankin, inda nan ne ta fi kamari a baya.

A domin haka, masana ke yin wani taro a ranar Talata a Abuja don sake yin nazari kan yadda za a yaki cutar.

Afrika dai tana da sauran shekaru biyu nan gaba kafin a bayyana ta a hukumance cewa ta tsira daga matsalar cutar Polio.