Sojoji sun damke dan uwan Shugaba Assad

Image caption Syria na cikin yakin basasa tsawon shekaru

An kama wani dan uwan shugaban Syria, Bashar al-Assad bisa zarginsa da hannu a kisan wani babban jami'in rundunar sojin kasar.

Rahotanni na cewa Suleiman Hilal al-Assad ya kashe kanar din ne a kan wata hanya.

An ce ya kashe sojan ne a gaban 'ya'yansa a kan hanyar zuwa birnin Latakia.

Wakilin BBC ya ce wata runduna ta musamman ta rundunar tsaron Syria ce ta kama Sulieman al Assad, a lokacin wani samame da ta kai a gidansu da ke kusa da Qurdaha, inda a can ne mahaifar su Assad din.

Rahotanni na cewa bai yi wata tirjiya ba a lokacin da aka kama shi.

Kisan dai ya janyo zanga-zanga a kasar, inda masu yin ta suka yi kira da a kashe Mr Suleiman al-Assad.