Masana na taro kan matsalolin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Govt
Image caption A baya-bayan nan shugaba Buhari ma ya gana da jami'an tsaron Najeriya

A ranar Talata ne masana kan fannonin rayuwa daban-daban a Najeriya suka fara wani taro a birnin Sokoto, domin tattaunawa kan kalubalen tsaro, da hadin kan kasa, da kuma ci-gaban da kasar ke samu a halin yanzu.

Ana sa ran masana daga manyan jami'oin kasar za su gabatar da kasidu fiye da 140 yayin taron na kwanaki biyu, wanda jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoton ta shirya.

Farfesa Sulaiman Khalid, shugaban tsangayar ilimin zamantakewar al'umma ta jami'ar, ya shaida wa BBC cewa makasudin taron shi ne duba neman mafita ga al'amuran da suka addabi kasa.

Ya ce suna sa ran gwamnati za ta yi amfani da shawarwarin da masana za su gabatar a lokacin taron domin warware matsalolin kasar.

Mahalarta taron sun hada da Malaman jami'o'i da sojoji da 'yan sanda da jami'an shige da fice Immigration, da jami'an hana fasa kwabri Custom, da kuma jami'an kula da gidan yari wato Prison services.

Taken taron shi ne "Tsaro, hadin kan al'umma da kalubalen ci-gaban kasa."