An gano sanadin gobarar Ghana

Hakkin mallakar hoto STEVEN ANTI
Image caption Gobarar Ghana

Wani kwamiti da gwamnatin Ghana ta nada domin gano sanadin gobarar da ta faru a kasar a ranar 3 ga watan Yuni, ya ce guntun sigari ne da aka jefe a kan tankar fetur ya jawo gobarar.

Gobarar -- ta faru ne a gidan man fetur inda mutane suka nemi mafaka sakamakon ruwan sama da ake tafkawa wanda ya jawo ambaliyar ruwa.

Jami'an tsaro suna tsare da mutumin da ake zargi da jefe sigarin, kuma ana bincikarsa domin a gano cewar ko da gangan ya aikata hakan.

A watan Yuni ne mummunar gobar ta afku, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 150 da asarar dukiyoyi.