'An kusa soma shari'ar barayin gwamnati'

Image caption Kwamitin ya gana da Buhari da kuma Jonathan kafin zaben 2015

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce nan da wasu 'yan makonni za a soma shari'ar mutanen da suka sace dukiyar kasa.

Shugaban ya bayyana haka ne a ganawar da ya yi da 'yan kwamitin wanzar da zaman lafiya wanda Janar Abdussalami Abubakar ke jagoranta.

Shugaban Buhari ya kara da cewa bayan gwamnati ta nemi a mai do da irin kudaden da aka sace aka kai bankunan kasashen waje, za kuma ta tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda suka sace irin wadannan kudade a gaban kuliya.

"Mun ci baya a cikin 'yan shekarun nan a matsayinmu na kasa, shi ya sa muke cikin matsalar tattalin arziki da kuma tsaro!" In ji Buhari.

A nasa bangaren, tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Janar AbdulSalami Abubakar ya bukaci shugaba Buhari ya tabbatar da bin doka da oda a kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa.