Ghana ta musanta iko da sararin samaniyar Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption John Dramani Mahma, shugaban Ghana

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Ghana ta musanta batun da shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya yi cewa Ghana ce take gudanar da sararin samaniyar Najeriyar.

Wannan martani da gwamnatin Ghana ta mayar dai ya biyo bayan wani umurni ne da ta ce shugaban na Nigeria ya ba wa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman na kasar da ta dauki matakin karbe ikon kula da sararin samaniyar Nigeria daga hannun Ghana.

Shugaban ya ce Ghana tana tafikar da sararin samaniyar Nigeria tun cikin shekara ta 1945.

A makon da ya gabata ne dai Muhammadu Buhari ya ba da umarnin bayan ya gana da manyan jami'an hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman kasar, a karkashin jagorancin sakatariyar din-din-din, Hajiya Binta Bello a fadarsa da ke birnin Abuja.