"Gwamma in mutu a teku a kan in mutu a Libya"

Kalaman Christiana mai shekaru 24 kenan, a lokacin da ita da mijin ta Samuel suka fito daga samfirin jirgin ruwa na MSF, mai suna Dignity 1.

Ta tsallake rijiya da bana saboda tana dauke da juna biyu na wata takwas.

Shekaru uku da suka wuce, suka tafi Libya domin neman rayuwar da ta fi wacce suke yi a Najeriya kyau.

Sai ta bude shagon gyaran gashi inda take gyarawa matan gari da matan 'yan ci-rani gashi.

Amma kuma bayan da tashe-tashen hankula da ake yi a Libya ya yi kamari, sai ta shawo kan Samuel ya bar kasar ya tafi kasashen waje.

A hanyar tafiyarsu, sai da aka rufe musu idanuwa daga Benghazi zuwa Tripoli. Inda suka yi tafiyar sama da kilomita 1000 babu ruwa babu abinci.

Daga nan ne kuma aka mika su zuwa wata kungiyar 'yan safarar mutane, wadanda suka dauki sa'o'i da dama suna tifaya inda su ka kai su gabar wani teku inda babu kowa suka ajiye su.

'Masu safarar mutane'

A nan ne suka ga wasu 'yan safarar mutane da jiragen ruwa guda uku.

Sai aka umurce su su shiga cikin jiragen ruwan kuma da tsakar dare jiragen suka fara tafiya.

Amma kuma a nan cikin tekun muka bar 'yan smoga.

"Sai suka rika ce mana ku ci gaba da bin wannan hanyar zaku samu taimako."

Bayan mun shafe sa'o'i muna tafiya cikin ruwa, sai kawai jirigin ruwa ya fara yoyyo.

To a wannan lokaci ne matan da suke cikin jirgin suka fara kuka kuma kawo ya yi tsoron cewar karshen tafiyar kenan.

Amma kuma da muka yi sa'a, sai wasu masunta da suke cikin jirgin ruwansu suka hange mu sai suka kawo mana agaji.

Kuma suka aike da sako zuwa wurin masu tsaron gabar tekun Italiya wadanda suka aike da jirgin ruwa na ceton mutane samfirin na kungiyar MSF mai suna 'Dignity 1'.

'Aikin Ceto'

Bayan da jirgin ruwan ya isa bakin tekun, a lokacin yana dauke da 'yan ci-rani 316 wanda masu aikin agaji suka kubutar daga tekun bahar-rum.

Christiana tana daya daga cikin mata 36 da Allah ya yi wa gyadar dogo.

Da akwai yara hudu a jirgin kuma karamin cikinsu mai watanni uku ne.

Sun ba da labarin duka da fyade da yin garkuwa da su da kuma daure su a gidan yari a lokacin da suke Libya.

Bayan sun iso wurin tarbar jiragen ruwa na Vibo Valentia wanda ke kudu maso yammacin gabar da ke kan bangaren kasar Italiya, sai aka yi mata rigista kuma aka kai ta asibiti domin a binciki lafiyarta.

An hada ta da wasu mata hudu a motar daukar marasa lafiya wadanda suka nema da kansu a yi musu gwajin kwayar cutar HIV saboda a lokacin da suke Libya, an yi musu fyade.

Bayan sa'o'i biyu sai ta dawo da labari mai dadi.

Lafiyar jaririn da ta ke dauke da shi kalau. Mace ce za ta haifa kuma za ta saka mata sunan jirgin ruwan da ya ceto su watau 'Dignity'.

Bayan da aka bayyana mata wannan labari mai dadi, sai ta tafi cibiyar saukar 'yan ci-rani da ke kudu maso gabashin kasar Italiya domin ta jira haihuwa jaririya 'Dignity'.