'Yan adawa sun yi korafi kan zaben Niger

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Niger, Muhammadou Issoufou

Takaddama ta kaure a jamhuriyar Nijar tsakanin 'yan adawa da bangaren jam'iyya mai mulki bisa zargin tafka magudi dangane da zabubbukan da za a yi a shekara ta 2016 .

'Yan adawar na zargin masu mulkin ne da yin aringizo wajen rijistar 'yan kasar, wanda suka ce wata alama ce ta shirya magudi.

Su dai 'yan adawar suna zargin cewa mutanen da aka yi wa rijista a jihar Tawa sun fi adadin asalin 'yan jihar.

Sai dai bangaren jam'iyyar mai mulki ya yi watsi da wannan zargin yana mai cewa hakan ba shi da tushe ballantana makama.

A shekara ta 2016 ne za a gudanar da manyan zabuka a Jamhuriyar Nijar.