Amurka ta tuhumi masu kutse a kwamfuta

Masu kutse a na'urar kwamfuta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An saci bayanai fiye da dubu dari da hamsin a cikin shekaru biyar.

Hukumomi a Amurka sun tuhumi wasu mutane tara da aikata manyan laifuffuka bayan da masu kutse a na'urar kwamfuta suka saci bayanan wani kamfani kafin a wallafa bayanan a madadin masu hada-hadar hannayen jari.

Masu shigar da kara na gwamnati sun ce mutane da ake zargi a badakalar sun samun kusan dala miliyan dari a matsayin riba ta haramtacciyar hanya.

Daga cikin wadanda ake tuhuma har da masu kutse a na'urar kwamfuta, da masu hada-hada a kasuwar hannayen jari da kuma 'yan kasuwa.

Mutanen dai na zaune ne a Ukraine da kuma Amurka.

Ana kuma zargin su ne da satar bayanai fiye da dubu dari da hamsin a cikin shekaru biyar.

Haka kuma akwai wasu zarge-zarge da hukumomi suka gabatar akan mutanen tara hade da wasu mutane ashirin da uku da wasu kamfanoni dake Rasha da Malta da Faransa da kuma Cyprus wadanda ake zargi da hannu a badakalar.