Dan Nigeria zai sha daurin shekaru 22

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Babban kotun Amurka ta yankewa Lawal Olaniyi Babafemi hukuncin daurin shekaru 22.

Amurka ta yanke wa wani dan Najeriya hukuncin daurin shekaru 22 a gidan yari a bisa laifin goyon bayan kungiyar Al-Qaeda.

An yi wa dan Najeriya mai shekaru 35 daurin shekaru 22 a gidan maza bayan ya amsa laifin hannu ga aikin ta'addanci ranar laraba.

A baya dai, Lawal Olaniyi Babafemi ya taba rubuta wa Al- Qaeda waka mai sautin 'rap' a kasar Yemen.

An bude shari'ar Lawal ne a Amurka bayan an tuso keyarsa daga Najeriya, inda masu gabatar da karar suka sanar cewa Alkalin babban kotun na Amurkan, watau John Gleeson ne ya yanke masa hukuncin daurin.

An soma shari'ar tun a watan Afrilun bara, inda Lawal ya amsa laifin baiwa kungiyar Al-Qaeda goyon baya a kasashen Larabawa.

Lawal ya yi ta safara tsakanin Yemen da Najeriya tsakanin watan Junairun shekarar 2010 da watan Ogustan 2011, inda ya je aka masa horo akan amfani da manya da kananan makamai ciki har da AK-47.

Shi kuma a na sa bangare, ya taimaka wurin gyara masu rubutun turanci a shafukan su na yanar gizo.

A baya ma an kama wani dan Najeriya watau Farouk Abdulmutallab, wanda ya sanya bam cikin kayan sa da nufin kunar bakin wake a wani jirgin Amurka, a shekara 2009.