Likitocin Ghana sun kara wa'adin yajin aiki

Image caption Asibitoci a Ghana sun kasance cikin yanayin tausayi

Likitocin Ghana sun yanke shawarar kara wa'adin yajin aikin nasu har makwanni biyu nan gaba.

Wani shugaban kungiyar likitocin na Ghana, ya sanar wa manema labarai a taron da suka yi ran Jumma'a cewa, sun yarda a tsakanin su cewa zasu cigaba da yajin aikin har sai gwamnatin kasar ta tsara musu ingantaccen yananyi na aikin.

Yajin aikin nasu ya sanya gwamnatin kasar cikin mawuyacin hali na gudanar da shirin da Asusun bayar da Lamuni na duniya ya tsara mata na kawo daidaito a tattalin arzikin kasar, inda likitocin suka daina kula marasa lafiya.

Likitocin dai kusan 2800 ne suka shiga yajin aikin, bisa dalilan neman karin albashi da sauran batutuwan jin dadinsu da ma kayan aiki a asibitoci.