Soke takardar shaidar NCE a Najeriya illa ce - dalibai

Hakkin mallakar hoto wiki
Image caption Daliban kwalejojin ilimi sun yi bore

A Najeriya wasu dalibai na kwalejojin ilimi na cewa ba su amince da soke takardar shaidar ilimi ta NCE a makarantunsu da gwamnati ta yi ba, duk kuwa da mayar da makarantun zuwa jami'o'i.

Daliban wadanda ke cewa mayar da makarantun nasu jami'o'i abu ne da suka yi maraba da shi,amma soke takardar shaidar NCE koma baya ne ga ilimin kasar musamman na arewa.

Koken na daliban dai shi ne sabon tsarin zai sa yankin arewacin kasar ya zama koma baya idan aka kwatanta shi da yankin kudanci wanda ya yi tazara sosai a harkar ilimin zamani.

A kwanakin baya ne dai aka ayyana mayar da wasu kwalejojin ilimi a kasar zuwa jami'o'i,to amma daliban suka ce an biyo bayan hakan da ayyana soke takardar karatu ta NCE.