NNPC ya nada sabbin shugabanni.

Image caption Kamfanin mai na NNPC

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC ya nada Mele Kyari a matsayin sabon shugaban reshensa da ke kula da sayar da danyen mai.

A cewar kamfanin yayi hakan ne tare da amincewar shugaba Muhammadu buhari.

Wasu daga cikin sabbin nadin da ka yi sun hada da Mr Ahmadu Sambo, wanda ke kula da ayyukan rijiyoyin mai na NNPC da kuma nadin Mr Dafe Sejebor a matsayin mai kula da zuba jarin kamfanin NNPC din.

Anyi nade-naden ne a yayinda da kamfanin mai na kasar yace yana sake tsare-tsarensa ta yadda zai rage yawan kashe kudi da tarin ma'aikata da shugabanni ta yadda zai zamo ingantacen Kamfani.

NNPC na samun kusan rabi ko miliyan daya na gangar mai a kowacce rana wanda yake kasaftawa matatun mai na Najeriya ganga 445,000 a kowacce rana.